‘Yan sandan jihar Kano sun bayyana kame mutane casa’in da uku cikin mako ɗaya da ake zargi da laifuka daban-daban.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka a jiya a yayin wata zantawa da manema labarai.
Kwamishinan ya ce waɗanda aka kama ana zargin an ɗau hayarsu ne domin ta da zaune tsaye a yayin bikin rantsar da gwamnan Kano da kuma mataimakinsa.
Ya kuma bayyana cewa an samu waɗannan mutane da muggan makamai da kuma ta’ammali da makamai masu illar gaske da kuma yunƙurin amfani da makaman wajen gudanar da sace-sace da kuma kawo cikas ga rantsar da sabon gwamna da aka yi.
Kwamishinan ‘yan sandan ya tabbatar da cewa za a miƙa su ga kotu domin girbar abin da suka shuka da kuma zama izina ga ‘yan baya.