Zababben Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Engr. Abba Kabir Yusuf, ya bayar da Shawara ga dai daikon Jama’a da kungiyoyi da suke ci gaba da gine-gine a filaye mallakar gwamnati ciki da kewayen kano da suka hada da dukkanin Makarantu na Jiha da dukkan wuraren Addini mallakin jihar da asibitoci da makabartu da kuma kwaryar birnin Kano.
Zababben gwamnan ya yi mika wannan shawarar ta hannun kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, a ranar Alhamis.
Idan za a iya tunawa tun gabanin zaben gwamnan Kano yayin yakin Neman zaben gwamnan an jiyo Jagoran Jam’iyyar Sanata Rabi’u Kwankwaso na ikirarin rushe irin wadannan wuraren da gwamnatin Jihar mai ci ta gwamna Ganduje ta cefanar da su.