Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken na ci gaba da ziyararsa ta kwana biyu a Beijing babban birnin China.
Wannan ziyara ita ce ta farko da waji babban jami’in diflomasiyya daga Amurka ya kai China cikin kimanin shekara biyar.
Jami’an Amurka sun ce babban maƙasudin ziyarar shi ne tattauna alaƙar kasarsu da China, wadda ta ke zama mai tsami a kullum.
Ziyarar na zuwa ne watanni biyar bayan ɗaga ziyarar farko da Blinken ya shirya zuwa, bayan kama wani balabalan ɗin leƙen asiri da ake zargin na China ne a sararin samaniyar Amurka.