Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma DINO MELAYE ya mayar da martani kan ikirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, na shirin yin ritaya daga siyasa.
Melaye ya ce maganar cewa Atiku zai yi ritaya daga siyasa ya hada hannu da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu karya ce.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin yakin neman zaben Atiku da Okowa, ya tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba mai rike da tutar jam’iyyar PDP zai dawo kan sharafinsa.
Atiku ya zo na biyu a zaben shugaban kasa da aka kammala a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Sai dai ya yi ikirarin cewa an tafka magudi a zaben da aka yi.
Tuni dai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya garzaya kotu domin kalubalantar nasarar Tinubu.