Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya ce gwamnatin da ta gabata ce ta jefa ‘yan Nijeriya cikin matsin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu.
Inda ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta da laifi kan halin da ake ciki a halin yanzu domin kuwa ta gaji matsalolin da ake ciki ne a yanzu.
Sarkin Kano na 14, Sunusi II ya bayyana haka ne a wani sakon bidiyo da aka yaɗa ta shafin Instagram a karshen makon nan.
Ya kara da cewa ya
dade yana gargadi kan a gyara matsalolin da ya hango wa kasar, amma aka ki
gyarawa.
Tsohon shugaban Babban
Bankin Nijeriya ya ce duk wanda ya ce gwamnatin Tinubu ce ta jefa kasar nan cikin matsin da ake ciki a yanzu
“ya zalunce ta” saboda ba laifinta ba ne.
Ya ce mutane na ta rubuto masa wasika cewa ana yunwa a kasa amma ya yi gum da bakinsa.
Inda ya ce ya yarda ana yunwa, amma bai iya cewa komai ba, saboda ɗau shekaru yana gaya wa mutane cewa wannan wahalar na fuskanto
ƙasar nan.
Ya ce tun lokacin da ya ga an dauki hanyar da ba ta dace ba wurin tafiyar da tattalin arzikin Nijeriya ya san cewa a karshe wahala za a sha.
Sarkin ya tunawa al’umma cewa a yayin wani taro a Kaduna, lokacin shi Tinubu yana
zaune, inda y ace duk wani dan siyasa da ya ce wa al’umma ba za a
sha wahala ba, kada
a zabe shi.
Khalifan Tijjaniya ya
ce an shafe shekaru takwas ana rayuwa ta karya a Nijeriya inda ya ce an ci ba
shi a kasashen waje da cikin gida haka kuma babban bankin kasar nan ya bayar da ba shi na cikin gida kusan naira
tiriliyan 30.
“A gwamnatin da ta