Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajanta wa ‘ƴan kasuwar Singa bisa iftila’in gobara da ta tashi a kasuwar SHEKARAN JIYA.
Sarkin ya jajanta wa ƴan kasuwar ne ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya fitar yau.
Sanarwar ta ce, “Mai Martaba Sarki ya nuna damuwarsa matuka a lokacin da ya samu labarin tashin Gobarar”.
Haka kuma a cikin sanarwar, Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajanta wa ‘ƴan Kasuwar Kurmi da ta Rimi waɗanda su ma suka gamu da ifila’in gobara kwanakin baya.
Mai martaba Sarkin ya buƙaci ƴan kasuwar har ma da ƙungiyoyinsu da su ci gaba da yawaita yin adduo’o’i tare da ɗaukar matakan kare afkuwar irin wannan iftila’i a nan gaba.