Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar Hajiya Rabi Dantata, matar hamshakin dan kasuwa, mai taimakon jama’a a nan Jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata.
Shugaban, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, a jiya, ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai tausayi da taimakon marasa galihu da kuma sha’awar hidimta wa mutane.
Ta kuma kasance mai farin jini mai son raba duk abin da take da shi ga al’umma.
Shugaban Buhari ya yi addu’ar Allah ya jiƙanta tare da karɓi ayyukanta na alheri, ya kuma bai wa iyalan Dantata hakurin jure wannan babban rashi da aka yi da ma al’ummar Musulmi bakiɗaya.