Home » Shugaba Buhari Ya Yi Alla-wadai da Kashe-kashen da Ake a jihar Benue

Shugaba Buhari Ya Yi Alla-wadai da Kashe-kashen da Ake a jihar Benue

by Anas Dansalma
0 comment

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi a Jihar Benue, bayan kashe mutane da dama a unguwar Umogidi da ke Entekpa-Adoka ta ƙaramar hukumar Otukpo a jihar.

Shugaban ya buƙaci a yi duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Asabar, ya ce shugaban ya yi Allah-wadai da amfani da ta’addanci a matsayin makami a rikice-rikicen kabilanci,  tare da umartar lallai a gano maharan tare da maganinsu cikin gaggawa.

Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin, ya kuma umarci jami’an tsaro da su kara sanya ido a kowane fanni da kuma gaggauta duba yanayin tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.

Ko da a daren jiya,  majiyarmu ta samu rahotonni game da hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wa sansanin ‘yan gudun hijira da ke makarantar firamaren Mgban da ke ƙaramar hukumar Guma ta jihar Benuwai.

Inda mai ba da shawara game harkokin tsaro a yankin, Christopher Waku ya tabbatar wa da majiyarmu cewa maharan sun kashe mutane kusan 34 da ya ritsa da wata mace mai juna biyu tare da jikkata mutane 40.

Jami’in Hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ya tabbatar da faruwar al’amarin ta hanyar saƙon kar ta kwana, sai dai bai kai ga yin ƙarin haske ba kan al’amarin.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi