Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar nan, Bola Ahmad Tinubu, ya ayyana sunanayen wasu mutane uku a matsayin masu taimaka masa cikin ƙunshin gwamnatinsa wacce ta fara a yau.
Mutanen da shugaban ƙasar ya naɗa sun haɗa da:
Ambasada Kunle Adeleke a matsayin cif-furotakwal na shugaban ƙasa.
Sai kuma tsohon kwamishinan labarai na jihar legas, Dele Alake, a matsayin mai Magana da yawun shugaban ƙasa.
Na ukun shi ne Olusegun Dada a matsayin mashawarci na musamman ga shugaban ƙasa kan kafafen sada zumunta na zamani.
Ana sa ran cewa shugaban ƙasar zai kammala naɗe-naɗensa ne cikin kwanaki 60 kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada wanda ya haɗa da muƙaman da ke buƙatar sahalewar majalisun ƙasar nan.