Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa na gudanar da gagarumin bincike kan yawan ma’aikatan gwamnatin tarayya a ƙasar.
Mista Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban Bankin Duniya Mr. Ajay Banga wanda ya kai masa ziyara a fadarsa da ke Abuja,
Cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale, shugaba Tinubu ya ce za su gudanar da gagarumin bincike, tare da nazarin tsarin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Shugaban kasa Tinubu ya ce bai amince da adadin mutanen da ke kan rajistar albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya ba, shugaban ya kara da cewa a shekarun baya da yake gwamna ya fuskanci irin wannan matsala.
Tinubu ya ce gwamnatinsa a shirye take ta toshe duk wata kafa da kuɗaɗen gwamnati ke sulalewa.
Sanarwar ta ce za a gudanar da binciken ne domin gyara tsarin aikin gwamnati a ƙasar, tare da sauya dabi’un ‘yan ƙasar da kuma wayar da kan jama’a.
Haka kuma shugaban ya ce yanzu haka gwamnatinsa na gudanar da wani binciken na ƙwaƙwaf a babban bankin ƙasar, CBN.