Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkanin jakadun Najeriya da su dawo gida.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya fadi hakan a jiya Asabar a cikin wata sanarwa da babban hadiminsa kan yada labarai da hulda da jama’a, Alkasim Abdulkadir, ya tabbatar da cewa an kira dukkanin Jakadun Najeriya su dawo gida.
Surutun da aka fara yi game da janye jakadan Najeriya a Ingila ne ya sa ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya fito fili ya warware zare da abawa da cewa daukacin Jakadun Najeriya aka ce su dawo gida kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarta,
kuma dukkanin Jakadun Najeriya suna karkashin shugaban kasa wanda shi ne ke da ikon dawo da su daga kowace kasa.