Home » Shugaba Tinubu ya ware makudan kuɗaɗe domin farfaɗo da Arewa

Shugaba Tinubu ya ware makudan kuɗaɗe domin farfaɗo da Arewa

by Auwal Hussain Adam
0 comment
Tinubu

Sugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake ware wasu makudan kudade don sake gina yankin Arewacin Najeriya da ya sha fama da matsalar tsaro.Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ware Naira biliyan 50 wato Naira miliyan dubu 50 don sake gina Arewacin kasar da rashin tsaro ya ɗaiɗaita.

Shugaban ya ware kudaden ne musamman don Arewa maso Yamma da kuma maso Gabas wadanda suka fi fuskantar matsalar tsaro.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a fadar shugaban kasa a jiya Alhamis a Fadar shugaban kasar a yayin wata ganawa. Shettima ya ce gwamnatinsu ta himmatu wajen mayar da hankali kan hanyoyin da za a bi a kawo karshen matsalar tsaro.

Yayin jawabinsa, Shugaba Tinubu ya yi magana kan irin wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki tun bayan cire tallafin mai.

Ya ba da tabbacin cewa irin tsare-tsaren da ya ke kawowa za su taimaka wajen daidaita tattalin arzikin kasar wanda jama’ar Najeriya za su fi mora.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi