Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, zai bayar da shaida a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a gobe Alhamis, akan zargin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku ke yi wa hukumar INEC da Shugaba Bola Ahmad Tinubu.
Farfesa Yakubu zai bayar da shaidar ne a ƙarar da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ya shigar, inda yake ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya yi a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
A bisa roƙon da lauyoyin Atiku suka yi, an gayyato Farfesa Mahmood Yakubu domin ya bayar da shaida akan zaɓen wanda ake ta taƙaddama a kansa.
Haka kuma, ana saran zai bayar da wasu muhimman takardun zaɓe waɗanda za su taimaka wa ƙarar da Atiku yake yi.
Majiyarmu ta rewaito cewar, Mr Uche, wanda yake babban lauya ne ya sanar da lauyoyin INEC, Shugaba Tinubu da APC dangane da zuwan Mahmood da aka tsara domin hana aukuwar abinda zai iya kawo wa zaman kotun cikas.