Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya buƙaci shugabannin majalisar tarayya da su kawo tsare-tsare waɗanda za su taimaki Shugaba Tinubu ya cika alƙawuran da ya ɗaukarwa ƴan ƙasar nan.
Majiyarmu ta rewaitio cewa, sanata Adamu ya bayar da shawarar ne a lokacin da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya jagoranci ƴan majalisar zuwa gidansa da ke a Keffi cikin jihar Nasarawa.
Shugaban na jam’iyyar APC ya bayyana cewa hanya ɗaya da za a taimaki gwamnatin Shugaba Tinubu, ita ce tabbatar da haduwar kawunan mambobin majalisun guda biyu. Kuma za majalusun zasu iya sauke nauyin da ke kansu ne kawai idan sun haɗa kai dakuma aiki tare da ɓangaren zartaswa
Ya kuma ja hankalinsu kan cewa lokacin neman muƙami ya ƙare, yanzu lokaci ne na yin mulki da tabbatar da akwai fahimta mai kyau a tsakanin ɓangaren majalisa da na zartaswa.