Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin bayar da tallafi domin rage wa ’yan Najeriya radadin cire tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi.
Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) Mele Kyari ya tabbatar da cewa biyan tallafin mai da gwamnati ke yi ya zama tarihi, hasali ma ba a ware masa ko sisi ba a kasafin kudin bana baya ga na watannin shida na farko da zai ƙare a wannan wata.
Da yake bayani bayan ganawarsa da jagororin jam’iyyar APC mai mulki, Kyari ya ce a halin yanzu kamfanin NNPC na bin gwamnati bashin Naira tiriliyan 2.8 na tallafin man, don haka kamfanin ba zai iya ci gaba da biyan waɗannan irin kuɗaɗe ba.
A gefe guda kuma, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki matakan da za su hana cire tallafin man jefa ’yan kasar nan cikin karin matsin rayuwa.
Mukaddashin daraktan Amnesty International, Isa Sanusi, ne ya shawarci gwamnati kan ta yi hattara ka da matakin nata ya kara talauta ’yan kasar nan wadanda da yawa da kyar suke iya biyan kudin makaranta da na asibiti ga kuma cefanan gida.