Shugaba Kasar Najeriya ya amince da naɗa Khalil Suleiman Halilu a matsayin sabon shugaban hukumar bunƙasa Kimiyya da Ayyukan Injiniyoyi (NASENI).
Wannan sanarwa ta fito ne ta bakin mai ba wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan yala labarai, Ajuri Ngelale, a yau.
Malam Halilu, mai shekaru 32 zai riƙe wannan muƙami ne na tsohon shekaru 5 kamar yadda kudin tsarin tafi da hukumar na shekarar 2014 ya ayyana. Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sallami tsohon shugaban hukumar Dr. Bashir Gwandu as EVC/CEO of NASENI.