Yayin da al’umar musulmi ke murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammad (SAW), Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shattima sun bukaci al’umma da su yi wa kasar nan addu’o’i tare da koyi da kyawawa halaye na manzon tsira annabi Muhammad (SAW).
A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yada labaru, Ajuri Ngelale, Tinubu ya ce “Najeriya tana a wani lokaci mai muhimmanci na wanzuwarta, yayin da gwamnati ke daukan duk wasu matakai na ciyar da kasar gaba, ana bukatar tallafi daga al’umma ta hanyar nuna kishin kasa, da juriya da kuma addu’o’i.”