Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo da Ministoci 44 a Majalisar Zartarwa ta tarayya da Gwamnoni 28, za su fara bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu da wa’adinsu zai kare.
Bayyana Kadarori ga dukkanin masu mukaman gwamnati wajibi ne, kuma Hukumar Da’ar Ma’áikata ta ce a shirye ta ke za ta fara ba su fom domin su bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara da wa’adin su zai kare.
Wadanda za su karbi wannan fom din su ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnoni 28 da ministoci 44 da hadiman su, ‘yan majalisar dokokin kasa da na jihohi, da shugabanin kananan hukumomi kamar yadda aka tsara a kundin tsarin mulkin kasar.