Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisar wakilai wasikan neman a yi garambawul kan kasafin kudi na shekarar 2022 domin ba shi damar ciyo bashin naira biliyan 500 don samar da kayyaki na tallafi ga ‘yan Najeriya.
Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ne ya karanta wasikar shugaban a zaman majalisar na yau Laraba,
A cikinm wasiƙar ya bayyan cewar, shugaban ƙasa ya ce bukatar hakan ta zama dole domin bai wa gwamnati damar samar da kayayyakin tallafi ga ‘yan Najeriya domin rage musu radadin da cire tallafin man fetur ya jefa su ciki.
A wani labarin kuwa, Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnan Borno Babagana Umara Zulum a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja a yau laraba.
To sai dai har izuwa lokacinda muke hada labaran, babu wani cikakken bayani game da ganawar tasu.