Shugabannin Ƙungiyar Kano Leads – Da Ruwana – sun kawo ziya gidan rediyon nan da talabijin na Muhasa a yau Litinin, inda suka zo da buƙatun haɗa gwiwa a gudu tare a tsira tare.

Kano Leads Kungiya ce mai zaman kanta, ta waɗanda suka damu da cigaban Kano da Kanawa, kuma masu fafutukar ganin sun kawo canji mai ɗorewa a fannoni da dama da suka haɗa da ilimi, da kiwon lafiya, da tattalin arziki, da tsaro, da muhalli, da cigaban al’umma, da kuma samar da ababen inganta rayuwa.

Galibin ƴan ƙungiyar sun yi ritaya bayan sun sadaukar da kai sun bauta wa ƙasa tuƙuru, amma duk da haka sun jajirce wajen cigaba da taimaka wa al’ummarsu.

GA CIKAKKEN RAHOTON: