Gwamnatin Mulkin Soji ta ƙasar Burkina Faso ta sanar da cewa ta yi nasarar daƙile wani yunƙurin juyin mulki da aka yi a ranar Talata.
Mai magana da yawun gwamnatin sojin, Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo, ne ya bayyana hakan, inda ya ce jami’an da suka yi yunƙurin juyin mulkin kan kama da yawa daga cikinsu, sannan an tsunduma neman waɗanda suka tsere.
Sannan ana cigaba da bincike domin bankaɗo waɗanda suka kitsa juyin mulkin.
Rundunar sojin, ta ce wannan yunƙuri ba komai ba ne facce ƙoƙarin tsunduma ƙasar cikin wani mahuyacin halli.
A ranar 30 ga watan Satumbar shekarar 2022, Kaftin Ibrahim Traoré, ya karɓe iko bayan wani juyin mulki da ya yi ƙasa da watanni takwas da wani juyin mulki da ya kaow ƙarshen mulkin dimokraɗiyya a ƙasar.