Tag: sojoji

Labarai

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 26 a Borno

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe aƙalla ’yan ta’adda 26 tare da lalata babura 10 a wani samame da ta kai bayan daƙile harin da mayakan suka kai wa sojoji a Kukawa da ke Jihar Borno. Mai magana da yawun Rundunar Operation HADIN KAI, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana hakan a wata sanarwa da […]

Babban Labari

Sojoji sun ceto mutum 48 da aka sace a Zamfara

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutum 48 da aka yi garkuwa da su bayan sun fatattaki ’yan bindiga da suka kai hari ƙauyen Magami da ke Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara. Sojojin sun ce sun samu kiran neman agaji da sanyin safiyar Lahadi cewa wasu ’yan bindiga masu […]

Babban Labari

Sojoji Sun Cafke Shugaban ’Yan Bindiga A Zamfara

Dakarun Sojin Najeriya, sun kama Kachalla Halilu wanda ake zargin ɗaya daga cikin shugabannin ’yan bindiga ne a Jihar Zamfara. Rahotanni sun ce sojojin sun kama shi ne a wata kasuwar mako-mako da ke garin Shinkafi, bayan sun samu sahihan bayanan sirri game da inda yake. Majiyoyi sun bayyana cewa dakarun rundunar sojin yankin sun […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai