Rundunar ƴan sandan Jihar nan ta ce ta kama mutane 29 ɗauke da makamai da kayan maye a lokacin bikin Takutaha da aka yi a fadin birnin.
Rundunar ƴan sandan ta ce ta kama mutanen ne a wurare daba-daban a faɗin jihar nan.
A cikin bidiyon da Kiyawa ya yi bayani an ga makaman da rundunar ta baje a gaban wadanda aka kama a hedikwatar ƴan sanda dake Bompai.
Makaman sun haɗa da wuƙaƙe da almakashi da ɗan bida da adduna, haka kuma an kama tabar wiwi, kamar yadda SP Kiyawa ya bayyana a ƙarshen mako.