Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, karancin kudin Naira ya rage yawaitar sayen kuri’u da aka saba gani a zabukan kasarnan,
Karancin Naira dai ya haifar da matsaloli a fadin kasar nan, lamarin da ya sa al’umma da dama suka koka da yadda suka kasa siyan kayan masarufi.
Babban bankin na CBN, ya sha suka sosai kan wannan manufa, wadda da dama suka bayyana a matsayin bata lokaci kuma ba a aiwatar da ita ba.
Buhari ya shaida wa manema labarai bayan ya kada kuri’a a mazaɓarsa, inda yake cewa yana sane cewa babu kudin kamar a can baya a hannun mutane da za su yi amfani da su wajen murde zaɓe, kamar yadda suka saba yi.
Wannan jawabi ya fito ta bakin mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu wanda ya tabbatar da cewa wannan mataki ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da sahihin zaɓe da ake gani a yanzu.