Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor mai ritaya, ya ce samar da tsaro ga babbar ƙasa irin Najeriya abu ne mai wahala duk da za a iya yin hakan.
Janar Irabor ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar a wajen taron karramawar barin aiki da aka shirya masa a barikin soji na Mogadishu Cantonment da Abuja babban birnin ƙasar.
Ya ce akwai jan aiki mai yawa a gaban sojojin ƙasar na bai wa ƙasar tsaron da take buƙata.