Home » Tsohon Gwamnan Kano, Kwankwaso, Ya Mayar da Martani Ga Kalaman Ganduje

Tsohon Gwamnan Kano, Kwankwaso, Ya Mayar da Martani Ga Kalaman Ganduje

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Tsohon Gwamnan Kano, Kwankwaso, Ya Mayar da Martani Ga Kalaman Ganduje

Tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya ce sun tattauna da Tinubu kan yadda za a iya yin aiki tare, yace amma har yanzu ba su yanke shawarwari ba, sai bayan an ranstar da ‘yan majalisa za su ga yadda za a yi aiki tare.

Injiniya Rabi’u Kwankwaso ya kuma jadada cewa batun tayin mukami da Tinubu ya yi masa suna kan tuntubar juna, kuma hakan ba wai yana nufin zai sauya jam’iyya ba ne, domin yana da tabbacin cewa gwamnatin hadaka Tinubu ke magana a kai.

Kwankwason ya ce nan da mako biyu za a fahimci inda suka dosa da shawarar da suka yanke.

Sannan ya mayar da martani kan kalaman Ganduje da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa da sunyi tozali da babu mamaki ya “mari Kwankwaso”.

Tsohon gwamnan ya ce wannan kalamai barazana ce wanda babu wanda ya isa ya kalle idonsa da irin wadanan maganganu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?