Tsohon Mai Ba Wa Shugaban Ƙasa Shawara a Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Femi Adesina, ya ce, ya shirya karɓar mukamin mataimakin shugaban Jaridar The Sun, wanda ake sa ran zai fara aiki a ranar 1 ga watan Satumba.
A baya dai Femi Adesina ya riƙe muƙamin Edita a Kamfanin Jridar ta The Sun, a matakai daban-daban.
Wannan bayani, ya fito ne daga bakin Adesinan a yayin da yake tattaunawa da manema labarai, Inda ya bayya na cewar, Shugaban Kamfanin, Senator Orji Kalu, ya tabbatar da ba shi muƙamin.
Adesina ya ce a yayin da ya bayyana aniyarsa ta barin gidan jaridar a baya, Kalu ya shawarce shi a kan kada ya rubuta takardar barin aiki.
A maimakon haka sai ya ba shi damar ya je ya riƙe mukaminsa na Gwamnati, daga baya bayan ya gama, ya iya dawowa.