Home » Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Gen. Sani Abacha, Gen. Oladipo, Ya Rasu

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Gen. Sani Abacha, Gen. Oladipo, Ya Rasu

by Anas Dansalma
0 comment

Diya wanda ya taɓa yin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa na mulkin soja, ya rasu ya na da shekaru 78 a duniya.

Ya rasu tsakar daren wayewar garin ranar Lahadi a wani asibiti, a Legas. Jami’in yaɗa labarai na marigayin mai suna Olawale Adekoya ne ya fitar da sanarwar rasuwar a madadin iyalan sa.

Wata ‘yar mamacin kuma lauya mai suna Oyesinmilola Diya ce ta sa wa takardar hannu a madadin iyalan sa baki ɗaya.

An haifi Diya a ranar 3 Ga Afrilu, 1944 a Odogbolu, Jihar Ogun. Ya yi mataimakin Abacha daga 1994 zuwa 1997.

Kafin nan ya riƙe Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, kuma ya yi Gwamnan Soja a Jihar Ogun tsakanin Janairu 1984 zuwa Agusta 1985.

Ya na cikin waɗanda Abacha ya zarga da yunƙurin juyin mulki, inda aka yanke masu hukuncin kisa.

Sai dai kuma Abacha ya rasu kafin a zartas wa su Diya hukunci, wanda hakan ya sa hawan Janar Abdulsalami mulki ya sake su.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi