Daga: Isma’il Sulaiman Sani
Allah Ya yi wa tsohon dan wasan kwaikwaiyon nan na arewacin Najeria, Alhaji Usman Baba Patigi wanda da aka fi sani da Samanja Fama, rasuwa.
Samanja ya rasu ne cikin daren da ya gabata bayan jiyya da ya yi fama da ita; yana da shekaru 81.
Za a yi jana’izarsa da misalin karfe 10 na wannan safiya ta Lahadi a gidansa da ke Kabala Costain a Kaduna.
Allah ya jikansa da rahma.