Gamayyar Ƙungiyoyin ƙwadogo, TUC, ta gargaɗi gwammatin tarayya da ta guji janye tallafin man fetur a daidai wannan lokaci da ta ce talakawan ƙasar na cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki.
Ƙungiyar na ganin idan har gwamnatin ta janye tallafin farashin man, to hakan zai ƙara wa jama’ar ƙasar ɗimbin wahalhalu da kuma matsin tattalin arziki.
Inda ita Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon suka ce sam ba za su lamunta ba.
A tattaunawarsa da manema labarai mai magana da yawun Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadagon, Kwamared Nuhu Toro, ya ce babu yadda za a yi a cire tallafin ba tare da an zauna an tattauna batun cire tallafin tsakanin masu ruwa da tsaki ba da su ba.
Ya ce matuƙar aka cire tallafin man to farashinsa zai yi tashin gwauron zaɓi, abin da kuma zai shafi farashin sauran kayayyaki a ƙasar.
Kwamared Toro ya ce cire tallafi ba shi ne mafita wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar ba.