Uwargidan shugaban kasar nan ta ce al`ummar Najeriya za su amfana daga fa`idar shirin farfado da rayuwar iyali da ta kirkiro da shi Mai dakin shugaban kasar Sanata Oluremi Tinubu ta tabbatarwa `yan Najeriya cewa zasu samu amfanu karkashin shirin da ofishinta ya bullo da shi mai taken farfado da rayuwar iyali da zarar shirin ya fara aiki gadan-gadan.
Ta tabbatar da hakan ne a jiya juma`a 7 ga wata a ofishinta dake fadar shugaban kasa yayin taro karo na biyu na shugabannin hukumar gudanarwar Shirin.
Uwargidan shugaban kasar wanda itace shugabar Shirin na kasa baki daya tace an rigaya an samar da dukkan matakan da suka kamata domin samun nasarar gudanuwar Shirin a daukacin jahohi kasar 36 har da birnin Abuja.
Ta ce Shirin zai yi naso har zuwa kananan hukumomin kasar, kuma yana dauke da aikace aikace daban daban da suka kunshi aikin gona, kiwon lafiya, ilimi, kyautata rayuwa da kuma samar da abubuwan da za su inganta tattalin arzikin jama`a.