Home » Wakar Ranar ‘Yancin Kan Nijeriya

Wakar Ranar ‘Yancin Kan Nijeriya

by Halima Djimrao
0 comment
Ranar 'Yancin Kai: Gwamnatin Tarayya ta ba da hutu

Rana ta ‘Yancin Kanta yau ta zago
Murna suke yau har da ɗaura agogo

Ban ce a dena hakan ba, ko kwa a fasa
Ga tambayoyi nan a kawo amsa

Yau shekaru sittin ku ƙara ukun kai,
Mulkin, ina wani ci gaban da ake kai?

Fannin kwarafshin kun ga yai tsamari
Daga jami’ai, ‘yan ƙwadago da samari

Matsalar tsaro ku fito ku ba ni bayani
Yaushe kuke sa ran ta sauya makani?

Ku taɓo ruwan shan nan abokin aiki
Kullun ana ta saye da ‘ya’yan banki

Ba a batun NEPA, su gyara sun ƙi
Yau in akwai gobenmu ba lantarki

Har lafiyar nan wadda taz zama jari
Sai mai kuɗi ne ke ganin ta da sauri

Da uwa-uba ilimi, a wannan ƙarni
Duk ya fi ƙarfin ‘yan ƙasa wayyo ni!

Babban misalin nan ku duba su ASUU
Duk malamanmu na Jami’a an kar su!

Har ɗaliban ma kar ka so kallonsu
An sa su duk a cikin halin ni-‘yasu

Fanni na kimiyyarmu har da fasaha
Wani in ya hango sai ya yi mana “Haha”

Tsada ta kaya walla sai kai kuka
Kullun farashi sai ka ce hankaka

‘Yan kasuwa an takure su ku duba
Da ma’aikata ‘yan ƙanƙana har babba

Aiki na yi neman sa ya zama aibu
Har ma da kansu suke faɗa wai “babu!”

Yau dai abinci fa ya zamo ɗan Sarki
Yunwa tana tashe kuna kan mulki

Duk ci gaban da akai irin na su gayen
Nan ne da ke haƙa rijiya yen-yen-yen

Zan ɗan taƙaita kar na buɗe aiki
Amma ku yo nazarin salonsu na mulki

Ni ne Hassan ɗan Abdu nai muku waƙa
Ko Mai Bulawus, tsokacinmu na miƙa.


© Hassan Abdu Mai Blouse
mailto:hassanblouse1@gmail.com
08066303359
01 Oktoba, 2023

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi