Home » Wani Jami’in Sojan Ƙasar Nan Ya Harbe Abokan Aikinsa Har Lahira

Wani Jami’in Sojan Ƙasar Nan Ya Harbe Abokan Aikinsa Har Lahira

Rundunar Sojin Najeriya

by muhasa
0 comment

Rundunar sojin kasar ta tabbatar da shari’ar wani soja da ya harbe abokan aikinsa da kansa har lahira a sansanin Rabah, a Jihar Sokoto a ranar Lahadin data  gabata.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birigediya-Janar Onyema Nwachukwu ne, ya bayyana a birnintarayya Abuja inda ya ce an fara bincike kan lamarin.

Mwachukwu ya bayyana cewa, ba za a iya tantance halin da ake ciki a yanzu ba, tunda sojan da ya kashe abokan aikinsa shi ma ya harbe kansa har lahira.

Ya kara da cewa babban hafsan soji na 8 da kuma kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji Manjo-Janar Godwin Mutkut da wasu manyan hafsoshi sun ziyarci wurin lamarin ya faru.

Ga Wani Labarin: Kano: INEC Ta Cire Sunan Alhassan Ado Doguwa Daga Jerin Sunayen Zababbun ‘Yan Majalisa

Mwachukwu yace, kwanadan ya jajantawa sojojin da suka rasa abokan aikinsu a irin wannan yanayi mara dadi.

Kwamandan ya bukaci su da su zama masu kula da ’yan uwansu kuma su ba da rahoton duk wani abin da ya faru da abokan aikinsu don hana sake faruwar wata barnar ana gaba.

Mwachuku yace kwamandan ya kuma kara musu kwarin gwiwa da su kwantar da hankalinsu da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi