Wani matashi mai suna Osman Arshaas ɗan ƙasar Pakistan ya yi tafiyar kilomita 4000 domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Ya fara tafiyar ne daga Pakistanya, inda ya wuce Iran zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa kafin ya isa Saudiyya.
Ya ce ya gamu da ƙalubale mai yawan gaske musamman na yanayi.
“Kowane musulmi yana da burin zuwa Makka wata rana, domin ziyartar dakin Ka’aba,” in ji Osman.
Ya kara da cewa, “A lokacin tafiyata, na kan kwana a duk wani masallaci ko otal da na gani, amma yawanci ina kwana a kan tanti”.