A kalla mutane takwas ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da, da dama suka jikkata sakamakon ruftawar wani sashe na ginin Babban Masallacin Zariya da ke Fadar Zazzau a Jihar Kaduna.
Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamalli wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wadanda abun ya shafa suna tsakar sallar La’asar ne ginin Masallacin ya rufta kansu.
Gwamnan ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu, kuma Ya ba wa wadanda suka jikkata lafiya.
inda gwamnan ya sha alwashin gudanar da bincike kan musabbabin ruftawar masallacin mai dimbin tarihi.
Daga karshe gwamnan ya bayyana cewa, tuni tawagar wasu manyan jami’an gwamnati karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Balarabe Abbas Lawal suka isa Zariya domin duba halin da ake ciki da kuma gabatar da kwamitin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin.