Wasu Mahara sun kai hari gidan Ardon Birni da kewayen Zariya, Alhaji Shuaibu Mohammed inda suka halaka shi tare da ’ya’yansa guda 4 a daren Asabar.
Mai dakin marigayin, Mallama Halima Shu’aibu ta sanar da manema labarai cewa Maharan su 5 ne kuma sun fada masu gida ne da misalin karfe 10:00 na dare sannan suka tafi dakin Ardon inda suka kashe shi.
A cewarta daga nan ne sai suka bi daki-daki na ’ya’yan nasa su hudu, dukkansu magidanta, suka halaka su. Matar ta bayyana sunan ’ya’yan da aka kashe da suka hada da Adamu Shuaibu, Musa Shuaibu, Abubakar Shuaibu da kuma Haruna Ibrahim.
Halima ta kara da cewa bayan sun kammala kisan, sai kuma suka kora shanunsu kimanin guda 100. Shi ma da yake magana da manema labarai, daya daga cikin ’ya’yan Ardon da ya rage, Abdurrahman Shuaibu ya ce bayan sun gama da gidansu, maharan har ila yau sun kuma harbi mutane biyu a kan hanyarsu ta barin kauyen