Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu ya yi jan hankali kan tuggu da wasu yan adawa masu fushi da nasararsa ke kullawa don kawo cikasa ga mika mulki musamman a ranar 29 ga watan Mayu da za a rantsar da shi.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran sa festus keyamo ya fitar a ranar Asabar, 25 ga watan Maris, inda ya kara da cewa ,Tinubun ya ce wadanda ke son yin zanga-zanga ne ke son ganin ya kafa gwamnatin hadin gwiwa.
Tunibu ya ce abin da kawai suke so shi ne a samu zaman lafiya a kasa kuma ba shi da amfani cewa wasu mutane da ya kamata su san abin da ya dace amma kuma suna goyon bayan tashin hankali kuma su dage don cimma hakan.
Tinubu ya kuma gargadi yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da takwararsa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, kan yin zanga-zanga a titi yayin da suka shigar da kara a kotu