Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a nan Jihar Kano, ta hana gayyata ko kama tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje domin bincikarsa kan zargin karbar cin hanci da rashawa.
A ranar Alhamis ne dai Hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta ce ta aika takardar sammaci ga tsohon gwamnan a kan ‘bidiyon dala’.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar, na cewa ta gayyaci Ganduje ne domin ya je ya wanke sunansa game da binciken da ake yi.