Hukumar yaƙi da fataucin Bil’Adama Ta Tarayyar Turai ta hada kai da wata ƙungiyar shugabannin jami’an tsaro don tinkarar matsalar fataucin almajirai da ci da guminsu a jihar Katsina.
A wani ƙoƙari na yaƙi da fataucin ƙananan yara da neman kyautata rayuwar almajirai a Arewacin Najeriya, Hukumar yaƙi da fataucin Bil Adama ta Tarayyar Turai ta shirya wani taron bita na kwana ɗaya, wanda ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki wajen inganta rayuwar almajirai.
An shirya taron bitar ne da nufin magance wasu batutuwa masu sarƙaƙƙiya game da tsarin almajiranci, da kuma yadda suka shafi fataucin Bil Adama a Arewacin Najeriya, musamman waɗanda ake tursasawa yin abubuwan cin zarafi.
A nasa bangaren shugaban kungiyar masu yaki da fataucin yara Abdulganiyu Abubakar ya ce suna bakin kokarinsu wajen kare hakkin yara almajirai ,inda ya kara da cewa kididdigar baya-bayan nan daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka na nuna cewa ana fataucin yara almajirai don a saka su cikin wasu ayyuka na cin mutunci.