Mataimakiyar shugaban kula al’amuran daliban wata jami’a mai zaman kanta a kano ta bayyana cewa jami’ar na shirin zakulo hazikan dalibai ‘yan asalin Jihar, domin ba su gurbin karatu kyauta a matsayin gudummawa da karfafa gwiwa ga hazikan dalibai, domin tallafa wa kokarin gwamnatin Kano na bunkasa ilimi.
Jami’ar ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi a wajen bikin baja kolin al’adun gargajiya da aka shirya wa sababbin daliban da aka rantsar domin fara sabon zangon karatu.
Ta ce wannan bikin al’adun ya shafi nuna sutura da yadda kabilu daban-daban da ke kasar har da tsarin rayuwarsu da shugabancinsu wanda ya hada da Fulani, Yaroba, Hausawa, Ebo da Barebari.