Jami’ar dai mallakin wani malamin addinin Kirista mai suna Bishop David Oyedepo, mamallakin Majami’a ta Living Faith Church,
Jami’ar dai na shirin hana mata masu sanye da hijabi shiga cikin harabar makarantar domin rubuta jarrabawar gwaji ta JAMB a garin Otta da ke jihar Ogun.
Majiyarmu ta rawaito cewa ɗalibai matan an dakatar da su daga shiga makarantar saboda kawai suna sanye da hijabi.
Wannan na zuwa ne cikin wani bidiyo na minti ɗaya wanda majiyarmu ta samu inda kusan ɗalibai mata biyar ne sanye da hijabi ke tsaye an hana su shiga jami’ar saboda sun saka hijabi.
Wani mahaifi da ya raka ‘yarsa ya tabbatar wa da majirmu cewa, masu gadin makarantar Canaanland suka hana ɗalibai masu sanye da hijabi shiga makarantar saboda umarni da suka samu daga sama.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa, sai da hukumomin jarrabawar JAMB suka sa baki kafin a bar ɗaliban su shiga cikin harabar makarantar bayan shafe awanni da dama suna tsaye.
Wani ganau ba jiyau ba ya bayyana cewa yana jami’ar Convenant a ranar Juma’a, inda masu gadin suka buƙaci wata matashiya da ta cire hijabinta ko mayar da shi ɗankwali idan tana so ta shiga.
Tuni dai mutane da dama suka fara alla-wadai da wannan al’amari a dandalin Tuwita tare da neman Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a da ta magance wannan matsala kafin ranar rubuta jarrabawa ta ƙasa da ake shirye-shiryen yi.
Ita Ƙungiyar Kare Haƙƙin Masu Sanya Hijab (HRAI) da kuma Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulman Ƙasar Nan (MURIC), ta aike wa jarridar DailyTrust jawabai na Allah-wadai kan wannan al’amari tare da neman mahukunta su sa baki domin magance wannan matsala.