Home » Wata Kotu Na Tuhumar Donald Trump Da Biyan Wata ‘Yar Wasa Maƙudan Kuɗaɗe

Wata Kotu Na Tuhumar Donald Trump Da Biyan Wata ‘Yar Wasa Maƙudan Kuɗaɗe

by Anas Dansalma
0 comment

Tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump na fuskantar tuhume-tuhume kan zargin da ake masa na biyan wata tsohuwar ƴar wasan batsa Stormy Daniels kuɗi domin ta ɓoye mu’amalar da suka yi.

Tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump na fuskantar tuhume-tuhume kan zargin da ake masa na biyan wata tsohuwar ƴar wasan batsa Stormy Daniels kuɗi domin ta ɓoye mu’amalar da suka yi.

Ms Daniels ta yi iƙirarin cewa Mista Trump ya kwanta da ita, kuma ta karɓi kuɗi $130,000 daga hannun tsohon lauyansa kafin zaɓen 2016 domin kada ta fallas shi.

Daga baya an ɗaure lauyan, Michael Cohen, bisa wasu zarge-zarge.

Tsohon shugaban ƙasar ya musanta cewa ya yi lalata da Miss Daniels tun bayan zargin da aka yi masa a shekarar 2018.

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi