Matashiyar, Rukayat Motunrayo Shittu mai shekaru 26 kuma wacce ta tsaya takara a jam’iyyar APC ta kafa tarihi bayan lashe kujerar ‘yar majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Owode/Onire da ke ƙaramar hukumar Asa ta jihar Kwara.
A yayin da yake sanar da lashe zaɓen nata, jami’an tattara sakamakon zaɓen, farfesa Akeem Olasunkanmi, ya bayyana cewa Rukayat ta samu ƙuri’u dubu bakwai da ɗari biyar da ashirin da ɗaya
Wannan ne ya ba ta nasara kan abokin karawarta mai suna Abdullah Magaji na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u dubu shida da ɗari tara da hamsin da bakwai.
Rukayat dai ita ce matashiya mafi ƙarancin shekaru izuwa yanzu da ta yi nasarar lashe zaɓen ‘yar majalisar jiha a faɗin ƙasar nan na wannan shekara.
Kafin tsayawa takarar ta dai, Rukayat ma’aikaciyar jaridar intanet ce wacce ta ajiye aikinta tun a cikin shekarar 2022 domin shiga harkokin siyasa.
Majiyarmu ta rawaito yadda al’ummar yankin da ta za ta wakilta ke nuna farin cikinsu bisa wannan nasara da ta samu ta hanyar bin tituna suna shewa.
Ita Rukayat a nata ɓangaren ta gode wa al’umma abisa ba ta wannan dama da suka yi.