Shahararriyar ‘yar fim ɗin Kannywood, Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon ta maka wani mai suna Bala Musa a kotun majistare da ke kan hanyar Daura, a jihar Kaduna, inda take zarginsa da lafin ɓata suna.
Lauyan Hadiza Gabon, Mubarak Sani, ya bayyana cewa tauraruwar fim ɗin ta sha fama da baƙaƙen maganganu daga al’umma saboda zargin da wanda ta shigar ƙara ya yi kwanaki a kanta.
Ya ce da yawa daga cikin masu amfani da soshiyal midiya sun riƙa kiran wacce yake karewa a matsayin macuciya saboda ƙin auren Bala Musa da ta yi bayan karɓe masa kuɗi.
Lauyan ya ce wannan batu na karɓar kudin ƙarya ne.
Sai dai lauyan wanda aka maka a kotun, Naira Murtala, ya ƙi amsa laifin.
Nan take kuwa mai shari’a, Shamsudeen Sulaiman, ya tambayi ɓangaren da ke ƙarar ko suna da hujja da za ta tabbatar da wancan batu ƙarya ne kuma an ɓata wa wacce yake karewa suna.
Lauyan ya amsa da e, suna da shaida.
Daga nan mai shari’ar ya ba da belin wanda ake ƙarar bisa sharaɗin gabatar da mutane biyu waɗanda za su tsaya masa kuma wajibi su kasance mazauna jihar ta Kaduna kuma ma’aikatan gwamnati.
Sai mai shari’a ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 15 ga watan da muke ciki domin masu ƙara su gabatar wa da kotu da shaidunsu.