Tsohon mataimakin shugaban jam’iyar APC na ƙasa shiyyar arewa maso yamma Dokta Salihu Lukman, ya ƙara jaddada cewa take-taken neman ɗora tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyar na ƙasa, ya saɓa wa dokokin jam’iyar ƙarara.
Haka kuma Dokta Lukman ya bayar da hujjojin cewa akwai fa maganar duba sanin ya kamata da ɗabi’u na gari kafin a ce za a naɗa Ganduje shugaban jam’iyar APC na ƙasa.
Dokta Lukman ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya nisanta kansa da duk wata ƙumbiya-ƙumbiyar neman naɗa Ganduje shugaban jam’iyar APC.