Wani dan bindiga ya harbi wata ma’aikaciyar wucin gadi ta Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Miss Glory Effion Essien, a hanyarta ta zuwa Karamar Hukumar Bakassi don gudanar da aikinta a ranar zabe.
Baturen Zaben Jihar Kuros Riba, Farfesa Gabriel Yomeri ne ya bayyana hakan inda ya ce an kai ta asibiti tana karbar magani.
Gabriel ya bayyana rashin jin dadinsa da afkuwar lamarin, sai dai ya ce ya ji dadi da harbin bai lahanta mata lakar jikinta ba.
Wani ganau ya ce, “harsashin ya same ma’aikaciyar ne a lokacin da take cikin kwale-kwalen da ya nufi yankin Bakassi domin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki.
Inda bayan harbin ta da aka yi mata ta yanke jiki ta faɗi a sume inda aka yi gaggawar garzayawa da ita asibiti domin ceto ranta.