Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari gidajen kwanan ɗaliban Jami’ar dake Gusau, tare da sace ɗaliban da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Lamarin dai ya faru ne da asubahin Juma’ar nan, inda rahotanni ke cewa maharan sun kutsa gidajen kwanan ɗalibai uku a unguwar Sabon Gida da ke maƙwaftaka da jami’ar.
Bayanan na cewa ƴan bindigar sun samu nasarar kwashe kusan dukkanin ɗaliban da ke zaune a gidajen da ke daura da jami’ar.
Har yanzu dai hukumomi ba su yi ƙarin bayani kan lamarin ba.