Rahotanni na nuni da cewa a ƙasashe kamar Kamaru da Benin da Jamhuriyar Nijar farashin man fetur ya ninka kan yadda suka saba siya a baya kafin Gwamnatin Najeriya ta sanar da cire tallafin man fetur.
Wannan ta sa cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi ya shafi tattalin arziƙin ƙasashen da ke kewaye da ita da kuma raguwar ƙarancin cin kasuwar bayan fage ta ɗanyen man fetur ɗin da akan yi.
Domin bincike ya nuna cewa ana safarar man ta ɓarauniyar hanya zuwa wasu ƙasashe kamar Sudan da yankin Kasashen Afirka ta Arewa wanda hakan ke haifar da ƙarancin kuɗin shiga ga gwamnatin Najeriya.
Ko da a ƙasar Kamaru, wacce ke iyaka da Najeriya, al’ummar ƙasar na kokawa game da tasirin da cire tallafin man ke da shi ga rayuwarsu tare da roƙon shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da ya sake duba al’amarin.
Bincike ya nuna cewa da yawa daga cikin al’ummun a Kamaru ba su da gidajen sayar saboda al’ummar ƙasar Kamaru da dama sun dogara ne da man da suke samu da wajen masu yin fasa ƙaurinsa daga Najeriya.
Idan za a iya tunawa dai, a ranar 29 ga watan Mayun shekarar da muke ciki ne sabon shugaban ƙasa Bola Ahmad Tiinubu ya sanar da janye tallafin man a jawabinsa na farko.
Sannan ya sake nanata a niyarsa na cire tallafin man a ranar tara ga watan Yuni, inda ya tabbatar da cewa Najeriya ba za ta cigaba da ba wa wasu kasashen tallafin man da ‘yan ƙasarsa ba sa cin moriya ba.