‘Yan majalisar dattawa na arewacin Nijeriya sun nuna adawarsu da yunkurin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, na yin amfani da karfin soji a kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
Sun bayyana haka ne ranar Juma’a a yayin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rubuta wasika ga majalisar dattawan kasar yana neman amincewarta don daukar matakin soji kan dakarun da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a makon jiya.