Rundunar ƴan sandan jihar Filato ta bayyana cewa dakarun ta sun kama shanu 77 da aka sato daga jihar Bauchi. Rundunar ta ce daga Bauchi aka kwato shanun mallakin wani makiyayi, aka kora su zuwa karamar hukumar Wase dake jihar ta Filato.
Ƴan sandan sunce bayani suka samu cewa ƴan bindiga sun sace shannun Galadiman Yuli Duguri daga kauyen Gajin Duguri a karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi. Ƴan sandan suka ce da hadin gwiwar ƴan banga da mafarauta suka karɓe shanun 77 suka mayar wa mai su.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Filato Okoro Alawari ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a kuma ya yi kira ga mutane su riƙa gaggauta kai wa ƴn sanda rahoton duk wani abinda ba su yarda da shi ba.